ABNA24: Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma kara da cewa; Abin da yake da muhimmanci ga Iran danagne da Iraki shi ne manufofi da masalahar kasashen biyu, da kuma tsaro da daukaka da kyautatuwar al’amurra a kasar Iraki.
Ayatollahi Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; Ko kadan Iran ba ta da nufin tsoma baki a harkokin cikin gidan Iraki, ba kuma za ta yi hakan ba a nan gaba; Abin da Iran take so shi ne Iraki ta zama kasa mai daukaka, mai cin gashin kanta, kuma dunkulalliyar kasa guda.
Bugu da kari, jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya ce; Abu daya da Iran take adawa da shi shi ne duk wani abu da zai sa Iraki ta zama mai rauni.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce shakka babu manufar Amurka danage da Iraki, sabanin manufar Iran ce, kuma Amurkawa ba son ganin Iraki ta zama mai cin gashin kanta ta ke yi ba.
342/